
Bankin Raya Afirka, AfDB, ya ce Afirka na asarar akalla mata da yara 300,000 a duk shekara sakamakon hayaƙin itacen girki.
Dakta Akinwumi Adesina, shugaban AfDB ne ya bayyana haka a yau Litinin a wani taron liyafa da ƴan jarida gabanin taron shekara-shekara na bankin a Accra, Ghana.
Adesina ya ce mata sun fi samun illar hayaƙin itacen ne yayin ƙoƙarin yi wa mutane gida girki, inda su kuma yara ke kamuwa yayin taimaka wa iyayen nasu mata wajen girkin.
Ya ce tara daga cikin kasashe 10 da suka fi fuskantar matsalar sauyin yanayi na Afirka ne.
A cewarsa, nahiyar Afirka ce ta biyu wajen fuskantar matsalar sauyin yanayi a duniya.
Adesina ya ce sauyin yanayi yana kashe tattalin arzikin Afirka, yana mai cewa nahiyar na yin asarar dala biliyan 7 zuwa 15 sakamakon sauyin yanayi.
A cewarsa, ana sa ran adadin zai haura dala biliyan 50 a duk shekara nan da shekarar 2040.