Home Siyasa Idan na zama shugaban ƙasa, zan baiwa mata dama dai-dai da maza — Amaechi

Idan na zama shugaban ƙasa, zan baiwa mata dama dai-dai da maza — Amaechi

0
Idan na zama shugaban ƙasa, zan baiwa mata dama dai-dai da maza — Amaechi

 

 

 

Rotimi Amaechi, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyar APC, ya yi alƙawarin baiwa mata dama dai-dai da ta maza a gwamnatin sa idan har ya ci zaɓen shugaban ƙasa a 2023.

Amaechi ya yi wannan alƙawari ne a wata sanarwa, bayan ya kai ziyarar tuntuɓa a jihohin Benue, Gombe da Katsina.

A cewar sa, shi bai yarda da a baiwa mata kashi 35 cikin ɗari a muƙaman gwamnati ba, inda ya ƙara da cewa” sabo da mata sun fi maza kwazo da kuma ƙwaƙwalwa.”

Amaechi ya ƙara da cewa wakilan jam’iya masu zaɓe mata, su zaɓe shi sabo da idan ya ci, zai basu cikakkiyar dama a gwamnatin sa.

“Idan mu ka ci, mata za su samu dama saidai da ta maza. Babu wani wai kashi 35 cikin ɗari. Ba haka bane, kin fi maza basira,” in ji shi.