
Gwamnan jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin Najeriya, Douye Diri, ya yi Allah wadai da kisan wani mutum mai suna Michael Isaiah.
Lamarin ya faru lokacin da jam’iyyar hamayya ta PDP ke gudanar da zaben fid da gwani na ‘yan takarar kujerun majalisa a mazabar Ogbia da ke garin a karamar hukumar Ogbia.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Kola Oredipe, ya rattaba wa hannu ya ce bata-gari ne suka yi kisan domin tayar da zaune tsaye da haddasa tashin hankali a zaben fid da gwanin da aka yi a jihar.
Gwamnan ya yi kira ga jami’an tsaro su gudanar da bincike kan kisan, da tabbatar da an kama wadanda suke da hannu akai, da fuskantar shari’a da hukuntasu daidai da laifinsu.
Gwanma Diri dai ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan mamacin, da jaddada musu zai tabbatar da an hukunta wadanda suke da hannu a lamarin.
An kashe matashin mai suna Michael Isaiah da aka fi sa ni da suna Tompolo ba tare da ya aikata komai ba.