
Mustafa Lamido, ɗan tsohon Gwamna Sule Lamido na Jigawa, ya zama dan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP a zaben 2023.
Jami’in kula da zaben fidda-gwani Isah Ahmed ne ya bayyana haka lokacin da ya ke sanar sakamakon zaɓen a yau Laraba a Dutse.
Ahmed ya ce Mustafa ya samu ƙuri’u 829 daga cikin ƙuri’u 832 da aka kaɗa, inda ya ƙara da cewa Saleh Shehu, ya zo na biyu ba tare da ya samu ƙuri’a ko ɗaya ba.
Ya taya wanda ya lashe zaɓen da wakilan jam’iyyar da kuma ‘ya’yan jam’iyyar da yadda suka gudanar da zaɓen ba tare da an samu matsala ba.
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Babandi Ibrahim, ya ce jam’iyyar za ta yi bakin kokarinta wajen ganin ta gabatar da sahihin ɗan takarar kujerar gwamna a jihar, wanda zai taimaka wajen dawo da martabar jihar da aka rasa.
Mustafa ya bayyana farin cikinsa da nasarar da aka samu, yana mai cewa: “Na amince da wannan takara da gaske cikin tawali’u, imani da kuma jajircewa.
Ya bayyana zaɓen a matsayin tarihi.
“Yayin da muka shiga mataki na gaba na yakin neman zabe, ina rokon ku da ku amince da ni, ku yi aiki da ni, ku yi yakin neman zabe tare da ku zabe ni domin mu sake daukaka jihar nan. Kuma
ina mai kira a gare ku da ku fito kwan ku da kwarkwatar ku don zaben PDP.
“Ina kira gare mu da mu guji siyasar rarrabuwar kawuna da rashin hadin kai. Kare martabar shi ne sama da duk wani son rai.