
Hukumar Shari’ar ta Jihar Kano ta aurar da wasu da su ka musulunt, inda ta ɗauki nauyin bikinsu; ta sai musu gadaje da sauran kayan ɗaki da na kicin.
Daraktan Gudanarwa da Ayyuka na hukumar, Auwal Lamido, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Alhamis a Kano, inda ya ce Hukumar ta kuma warware wasu rikice-rikice bakwai da suka shafi rikicin shugabancin masallatai da makarantun Islamiyya cikin watanni biyu.
A cewar daraktan, an warware matsalolin a watan Maris da Afrilu.
Malam Lamido ya bukaci jama’a da su tabbatar da cewa su na aiwatar da ɗabi’u masu kyau da kuma tsoron Allah a cikin mu’amalarsu.
An kafa hukumar ne a shekara ta 2001 a matsayin ofishin kula da harkokin zamantakewa na Musulunci, amma sai a ka ɗaga likkafarta zuwa Hukumar Shari’a a ranar 7 ga Nuwamba, 2003.
Aikinta shi ne ingantawa, aiwatarwa da kuma inganta ɗabi’un Musulunci da na al’adu a cikin jihar.