Home Siyasa Ɗa ga Buhari, Fatuhu Muhammad, ya sha kaye a zaɓen-fidda gwani na APC

Ɗa ga Buhari, Fatuhu Muhammad, ya sha kaye a zaɓen-fidda gwani na APC

0
Ɗa ga Buhari, Fatuhu Muhammad, ya sha kaye a zaɓen-fidda gwani na APC

 

 

Fatuhu Muhammad, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Daura/Sandamu/Maiadua, ya sha kaye a zaɓen sa na sake tsayawa takara a jam’iyyar APC.

Muhammad, wanda ɗa ne ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ne, ya sha kaye a hannun Aminu Jamu a zaɓen.

Da yake bayyana sakamakon zaben a jiya Juma’a da daddare a sakatariyar karamar hukumar Daura, jami’i zaɓen, Bala Zango, ya ce Aminu Jamu ya samu kuri’u 117 inda ya zama wanda ya yi nasara.

Ya kara da cewa Fatuhu Muhammad ha zo na biyu da kuri’u 30.

A watan Oktoban 2018, wasu ’yan takarar mazabar Daura/Sandamu/Maiadua uku sun yi ƙorafin nuna rashin amincewarsu da zargin da ake yi wa Muhammad, inda suka ce jam’iyyar da gwamnatin jihar sun yi musu rashin adalci.

A wata sanarwar hadin gwiwa da ‘yan takarar uku, Salisu Daura da Aminu Jamu da kuma Kabir Abdullahi suka fitar, sun soki gwamnatin jihar da jam’iyyar da rashin adalci da son zuciya da kuma tauye tsarin zabe.