Home Labarai Kotu ta umarci MTN da NELMCO da su biya N200m ga yarinyar da wutar lantarki ta ja

Kotu ta umarci MTN da NELMCO da su biya N200m ga yarinyar da wutar lantarki ta ja

0
Kotu ta umarci MTN da NELMCO da su biya N200m ga yarinyar da wutar lantarki ta ja

 

 

 

A jiya Litinin wata Babbar Kotu a Jihar Yobe ta umarci kamfanin layin waya na MTN da Kamfanin kula da Diyya na Wutar Lantarki na Ƙasa, NELMCO da su biya Hamsatu Abdullahi naira miliyan 200 a matsayin diyya bisa sakaci da su ka yi.

Alƙalin kotun, M. Lawu Lawan ya ce mai ƙara ya gabatar da gamsassun shaidu na baki da kuma a rubuce a kan waɗanda a ke ƙara.

Ya kuma ƙara da cewa mai ƙarar na da hakkin a biya ta diyya duba da irin nakasar da ta samu na rasa duka hannuwanta da kuma kafarta ta dama.

“Hakan ya haifar mata da raɗaɗi, damuwa, bakin ciki, takaici da kuma zarya zuwa asibiti, gami da rashin samun ababan more rayuwa.

“Sabo da haka a haɗa hannu a biya mai ƙara Naira miliyan 200,” in ji alƙalin.

Tun da fari dai, kotun ta kama MTN da NELMCO da laifin kafa na’urar samar da sabis na waya mai karfin 33KV ba tare da wata kariya ba a jikin gidan su yarinyar ƴar shekara 4, lamarin da haifar da ta taɓa, inda wutar kuma ta ja ta, har ta yi sanadiyyar rasa hannuwanta da ƙafar dama.