Home Labarai Ƴan Sanda sun kama wani da sassan jikin mutum

Ƴan Sanda sun kama wani da sassan jikin mutum

0
Ƴan Sanda sun kama wani da sassan jikin mutum

 

 

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Zamfara ta tabbatar da kama wani mutum da a ka samu hannun ɗan’adam a wajensa a Ƙaramar Hukumar Zurmi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin, inda ya ce rundunar hadin gwiwa ta ‘yan sanda da sojoji ne su ka kama wanda ake zargin a wani samame na yaki da ‘yan fashin daji a yankin Dauran-Zurmi.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin dan haramtacciyar kungiyar yansakai ne, waɗanda su ke addabar al’ummar Dauran ta hanyar kai musu hare-hare basu ji ba basu gani ba.

Ya ce wanda ake zargin ya amsa cewa shi da sauran ’yan kungiyarsa uku, wadanda su ka tsere, sun kashe Abdullah tare da yanke hannunsa na dama.

SP Shehu ya bayyana cewa an fara gudanar da bincike domin kamo sauran wadanda ake zargin.