
Jagoran jam’iyar APC kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa kasa a jam’iyyar, Bola Tinubu ya ce an yi wa kalamansa a kan Shugaba Muhammadu Buhari mummunar fahimta.
Tinubu ya ce raina Buhari da wasu ke cewa ya yi ba ya daga cikin halayyarsa.
Tinubu ya tada ƙura a fagen siyasa a bisa cewa shi ya yi sanadiyar cin zaɓen Buhari a 2015 yayin da ya k3 ganawa da sa dalaget ɗin APC a jihar Ogun a ranar Alhamis.
A yayin taron, Tinubu ya ce ba don shi ba da Buhari ya faɗi zaben 2015.
Sai dai kuma a wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a, Tinubu ya ce bai fadi hakan da nufin yi wa Buhari rashin ladabi ba.
Ya ce da yawa ko dai ba su fahimci kalamansa ba ko kuma sun yi musu wata fassara ta daban.
Tinubu ya ce “Ina alfahari da kaina kan rawar da na taka a nasarar da APC ta sha yi. Amma tabbas Shugaba Buhari shi ne babban jagoran nasarar. Sau biyu ana zabarsa a matsayin shugaban kasa.
“Ya jagoranci kasar nan tsawon shekara bakwai, babu mai karyata hakan.
“Ban isa na raina abin da ya yi ba ko raina matsayinsa a APC da Najeriya ba,” in ji Tinubu.