
Sanata mai wakiltan Kebbi ta tsakiya, Adamu Aliero, a yau Alhamis ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar PDP.
Da yake sanar da sauya sheƙar ta sa a Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi, Aliero ya ce ya yanke hukuncin ne sakamakon kokarinsa na cika burin ɗimbin magoya bayansa da suka yaɗu lungu da saƙo a faɗin jihar.
Aliero ya yi gwamnan jihar Kebbi na wa’adi biyu, kuma ministan babban birnin tarayya, FCT, kuma yanzu haka sanata ne mai ci.
Sanatan ya ce: “Ni, Muhammadu Adamu Aliero, al’ummar mazaba ta, wato Kebbi ta Tsakiya da ɗumbin magoya baya na daga fadin jihar Kebbi, na yanke shawarar sauya sheka daga APC zuwa PDP saboda rashin adalcin da muka sha a tsohuwar jam’iyyarmu ta APC.
“Wadanda ke goyon bayan akidar siyasa ta, an yaudare su kuma an yi musu rashin adalci, don haka akwai bukatar mu bar jam’iyyar zuwa wata jam’iyyar siyasa inda muke ganin za a karɓe mu hannu biyu-biyu a yi mana adalci.”
A cewarsa, kafin ya kai ga kammala ficewa daga jam’iyyar, ya yi kokari da dama don warware matsalolin da ya ke fuskanta, har ta kai ga ya shigar da korafi zuwa shelkwatar jam’iyyar ta kasa amma duk da shugabannin jam’iyyar sun shiga maganar, babu wani abin kirki da ya fito daga cikinta.
Don haka ya yi kira ga daukacin magoya bayansa na gundumar Kebbi ta tsakiya da kuma sauran magoya bayansa a fadin jihar da su zabi jam’iyyar PDP domin tabbatar da nasarar ta a kowane mataki.