Home Labarai Ƴan bindiga sun sun ɗauke ƴan kasuwa 40 a titin Sakkwato zuwa Zamfara

Ƴan bindiga sun sun ɗauke ƴan kasuwa 40 a titin Sakkwato zuwa Zamfara

0
Ƴan bindiga sun sun ɗauke ƴan kasuwa 40 a titin Sakkwato zuwa Zamfara

 

Wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton ƴan fashin daji ne, a jiya Asabar sun yi garkuwa da mutane kusan 40 a hanyar Zamfara.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa mafi akasarin wadanda lamarin ya rutsa da su ƴan kasuwa ne masu safarar wayoyin hannu da sauran kayayyaki masarufi a Kasuwar Bebeji da ke jihar Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun tare matafiya sama da 60 da suke dawowa daga Ƙaramar Hukumar Tambuwal a jihar Sokoto amma 20 sun yi sa’ar tserewa daga harin.

Shugaban kungiyar ƴan kasuwar, wanda ya tabbatar wa BBC harin ya ce lamarin ya faru ne a kusa da Kureka da kauyen Bakura.

Ya ce kimanin mutane 40 ne ke cikin wata motar bas ta Coaster, yayin da 18 daga cikinsu ke cikin wata motar ƙirar Hiace.

Kakakin Rundunar Ƴan Sandan Jihar Zamfara SP. Muhammad Shehu ya tabbatar da faruwar harin, ya ce ana ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro na hadin gwiwa domin gano inda a ka kai ƴan kasuwar da kuma kubutar da su.