Home Labarai Majalisar dokokin Kano ta naɗa sabon mataimakin shugaban masu rinjaye

Majalisar dokokin Kano ta naɗa sabon mataimakin shugaban masu rinjaye

0
Majalisar dokokin Kano ta naɗa sabon mataimakin shugaban masu rinjaye

 

 

 

 

A jiya Talata ne dai Majalisar Dokokin Jihar Kano ta naɗa Magaji Zarewa a matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye, bayan da Abdullahi Yaryasa ya yi murabus.

Yaryasa ya yi murabus ne bayan ya fice daga jam’iyyar APC, zuwa jam’iyyar New Nigerian Peoples Party, NNPP.

Shugaban majalisar, Hamisu Chidari, wanda ya karanta wasiƙar murabus ɗin Yaryasa a zauren majalisar, ya yi masa fatan alheri a sabuwar jam’iyyarsa tare da gode masa bisa ɗumbin gudunmawar da ya bayar a majalisar.

Chidari ya kuma taya Zarewa, mai wakiltar mazaɓar Rogo murnar naɗin da aka yi masa tare da ba shi tabbacin goyon bayan majalisar.

Malam Zarewa ya yaba wa ƴan majalisar da suka ga cancantar sa kuma su ka zaɓe shi a matsayin sabon mataimakin shugaban masu rinjaye.