
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin sa ta samu ci gaba sosai a kan alkawuran da ta ɗauka na magance matsalolin tsaro da cin-hanci, inda ya ce ta kuma bunƙasa tattalin arziki.
Buhari ya bayyana hakan ne a bikin yaye ɗaliban kwalejin horon ƴan sanda da ke Wudil a Jihar Kano a yau Alhamis.
A cewar Buhari, tuni gwamnatinsa ta ci ƙarfin Boko Haram, IPOB, ESN da kuma fashin daji, inda ya ƙara da cewa gwamnatin na ƙara ƙoƙarin magance matsalolin tsaron.
Shugaban ya ƙara da cewa gwamnatin sa ta magance cin hanci, inda ya ce ya yi ƙoƙari sosai domin ganin ƙasar bata koma lokacin gwamnatocin baya ba kan matsalar cin-hanci da rashawa.
Buhari ya ƙara da cewa tuni al’ummomin da Boko Haram da fashin daji ya yi sun fara koma wa ƙauyuka da garuruwan su.
A nashi jawabin, Shugaban kwalejin, AIG Abdurrahman Ahmad ya yaba wa gwamnatin taraiya da sauran masu ruwa da tsaki bisa taimako da takkafin da su ke yi ga makarantar.
Sai dai kuma shugaban makarantar ya ce kwalejin na fuskantar tarin matsaloli da sai gwamnati ta shigo domin magance su.