
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya miƙa sunayen ministoci domin maye guraben waɗanda suka sauka da wadanda ya sauke daga kan mukamansu.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Ahmed Lawan ne ya karanta wasikar mai ɗauke da sunayen mutane bakwan domin sahale wa da naɗa su a matsayin ministoci a yau Talata.
Sunayen sun hada da Ibrahim El-Yakub daga Jihar Kano, Umana Okon Umana (Akwa Ibom), Henry Ikechukwu Iko (Abia), Ademola Adegoroye (Ondo), Odum Odi (Rivers).
Sauran su ne Goodluck Nnana Opia (Imo) da kuma Joseph Ukama (Ebonyi ).
Sanata Lawan ya ce nan gaba za su tantance sunayen da aka mika musu domin tabbatar da su ko kuma akasin haka.
A watan Satumbar 2021 ne Shugaba Buhari ya sauke Ministan harkokin Gona, Alhaji Sabo Nanono da Ministan Ma’aikatar Lantarki, Injiniya Saleh Mamman ba tare da bayyana wani dalili ba.
Kazalika a watan jiya ya umarci ministocinsa da ke son tsayawa takarar siyasa su sauka daga mukamansu.