
Sanatoci uku na jam’iyyar APC sun yi murabus daga jam’iyyar mai mulki.
Sanatocin sun haɗa da: Ahmad Babba Kaita (Katsina ta Arewa), Lawal Gumau (Bauchi ta Kudu) da Francis Alimikhena (Edo ta Arewa).
Sanarwar murabus dinsu da sauya shekar ta su na ƙunshe ne a cikin wasiku da ko wannen ya aike wa shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan ya kuma karanta yayin zaman majalisar a yau Talata.
Yayin da Kaita da Alimikhena suka sauya sheka zuwa babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Gumau, ya koma jam’iyyar NNPP.