Home Labarai Ba za mu iya sayar da man fetur ƙasa da N180 ba — IPMAN

Ba za mu iya sayar da man fetur ƙasa da N180 ba — IPMAN

0
Ba za mu iya sayar da man fetur ƙasa da N180 ba — IPMAN

 

 

Ƙungiyar Dillalan Man fetur ta Ƙasa, IPMAN ta ce ta fara sayar da duk lita daya ta mai tsakanin N170 zuwa N190 tana mai cewa abu ne mai wahala su iya ci gaba da sayar da shi kan naira 165.

Jaridar The Nation ta ambato Sakataren IPMAN, reshen Legas Akeem Balogun na cewa ”lura da yadda kasuwar take a yanzu, babu yadda za a yi mu sayar da mai kasa da naira 180 a duk lita”.

Ya kara da cewa ”duk wani mamba da wata hukuma ta hana yin haka ya yi gaggawar sanar da uwar kungiya.”

An shafe watanni ana wahalar mai a Najeriya, musamman a manyan biranen kasar da suka hada da Abuja da Lagos.

IPMAN reshen na jihar Legas, ta ce rufe gidajen man wasu mambobinta ya kara haifar da dogayen layuka musamman a Lagos da Akure da Ado-Ekiti da Abeokuta da Jos.