Home Labarai Har yanzu akwai ƴan matan Chibok 20 a Sambisa, in ji waɗanda su ka kuɓuta

Har yanzu akwai ƴan matan Chibok 20 a Sambisa, in ji waɗanda su ka kuɓuta

0
Har yanzu akwai ƴan matan Chibok 20 a Sambisa, in ji waɗanda su ka kuɓuta

 

 

 

Biyu da ga cikin ƴan matan Chibok da su ka kuɓuta a hannun ƴan Boko Haram bayan sun yi garkuwa da su a 2014, sun bayyana cewa har yanzu a kwai sama da ƴan matan 20 a hannun ƴan ta’addan.

Mary Dauda da Hauwa Joseph, ƴan matan biyu da aka ceto daga GGSS Chibok da ke Borno a shekarar 2014, sun bayyana haka ne ga manema labarai a jiya Talata a Maiduguri, a wani taron manema labarai da aka gudanar a Bataliyar Sojoji ta Kwamanda Maimalari.

Ƴan matan sun bayyana cewa sama da wasu 20 da suka bace suna nan a sansanin Gazuwa da ke dajin Sambisa, shekaru takwas bayan sace su da mayakan Boko Haram suka yi.

Sansanin Gazuwa ya yi shura a matsayin Shelkwatar kungiyar ta Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād, tsagin Boko Haram, wanda a da ake kira Gabchari, Mantari da Mallum Masari, mai tazarar kilomita 9 zuwa karamar hukumar Bama a Borno.

A yayin hira da manema labarai, Mary da Hauwa sun bada labarin yadda su ka kuɓuta da ga sansanin ƴan ta’addan cikin wani yanayi na wahala.