
Wata Kotun Majistare mai lamba 60, ƙarƙashin Mai Shari’a Tijjani Sale .injibir, ta haramtawa wani matashi hawa doki na tsawon shekara uku.
Matashin, mai suna Abdulsalam Bashir ya gurfana a kotun ne sakamakon ture wata mata da doki har ta samu munanan raunuka.
Bayan hukuncin haramta hawa dokin, alƙalin ya yanke wa matashin, ɗan unguwar Sabuwar Ƙofa da ke a Kano hukuncin zaman gidan yari na shekara ɗaya, ko zaɓin biyan tarar naira dubu 25.
Ya kuma umarci mai laifin da ya biya kuɗin magani naira dubu 100 ga matar.