
Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ɗaya daga cikin kurakuran da ya tafka a rayuwarsa shi ne zaɓar mataimaki a 1999.
Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyar PDP, Atiku Abubakar, shi ne ya yi wa Obasanjo mataimaki a lokacin da ya mulki ƙasar nan a tsarin demokradiyya daga 1999 zuwa 2007.
Da yake amsa tambayoyi a wani taro na wasu ɗalibai a Abeokuta da ke Jihar Ogun, kamar yadda jaridun Najeriya suka ruwaito, Obasanjo ya ce “ba zan ce bana kuskure ba – Na yi su da yawa.”
“Amma wani abu da ya faru da ni shi ne Ubangiji bai taɓa kunyata ni ba. Kuma wannan abu ne mai muhimmanci.
“Misali, ɗaya daga cikin kurakuran da na yi shi ne ɗaukar mataimaki lokacin da zan zama shugaban ƙasa.
“Sakamakon wannan kuskure ne mai kyau, Ubangiji ya kare ni,” in ji Obasanjo.