Home Labarai Yara 3,000 ba sa zuwa makaranta sakamakon ta’adar fashin daji

Yara 3,000 ba sa zuwa makaranta sakamakon ta’adar fashin daji

0
Yara 3,000 ba sa zuwa makaranta sakamakon ta’adar fashin daji

 

 

A ƙalla yara 3,000 ne wasu ƴan bindiga su ka kora daga makaranta a wasu ƙauyukan Ƙaramar Hukumar Jibia ta Jihar Katsina.

Sa’ad Salihu, shugaban sansanin ‘yan gudun hijira ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara da manema labarai suka kai yankin a jiya Litinin.

Salihu, wanda kuma shi ne shugaban Ƙungiyar Ci gaban Matasa ta Shimfida, ya ce wasu daga cikin yaran su na zuwa makaranta kafin al’ummar yankin su tsere sakamakon hare-haren ƴan fashin jeji.

Ya bayyana cewa da yawa daga cikin ƴan gudun hijirar, waɗanda a halin yanzu su ke makarantar sakandiren ƴan mata ta gwamnati a Jibia, sun fito ne daga al’ummomin Kwari, Zango, Shimfida, Tsauni, Far Faru, Tsambe da Gurbin Magariya.

A cewarsa, babban koma-baya ne a fannin ilimi, sakamakon yawan yaran da ƴan fashin jeji su ka kore su daga makaranta, inda ya ce sama da ‘yan gudun hijira 15,000 ne a sansanin.

“A ƙalla mata da kananan yara 23 ne su ka mutu a sansanin a cikin watanni huɗu, ko dai sakamakon hauhawar jini ko kuma damuwa, yayin da mata 35 su ka haihu.

“Sama da yara 3,000 da ke sansanin a halin yanzu ba sa iya samun ilimi a halin yanzu.”

“Daga al’ummar Shimfida kadai, muna da mutane 8,000 da ke wannan sansanin; Al’ummar Far Faru, sama da 7,000 da kusan 200 sun fito ne daga al’ummar Zango.