
Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA, reshen jihar Neja, ta ce za ta sa ƙafar wando ɗaya da ƴan siyasa masu ƙarfafa wa matasa gwiwar shan miyagun ƙwayoyi a lokacin yaƙin neman zaɓe.
Haruna Kwetishe, Kwamandan NLDEA na jihar, ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Talata a Minna cewa za a kama irin waɗannan ƴan siyasa tare da gurfanar da su a gaban kuliya.
“Za mu sanya ido kan duk wani taron siyasa tare da kama duk wani shugaba da aka samu yana rabawa matasa miyagun kwayoyi a lokacin gangamin siyasa.
“Ba za mu amince da duk wani nau’i na rigingimun siyasa da dabanci a lokacin yakin neman zabe da bayan yakin neman zabe ba.
“Za mu tabbatar da kamawa tare da gurfanar da duk wani mutum ko gungun mutanen da aka samu suna raba wa matasa miyagun kwayoyi a duk wani taron siyasa a jihar,” in ji kwamandan.
A cewarsa, rundunar za ta tura jami’an farin kaya zuwa wuraren yakin neman zabe domin sa ido da daukar matakan da suka dace a inda ya dace.
Kwetishe ya ce rundunar ta haɗa kai da dukkan hukumomin tsaro domin magance shaye-shayen miyagun kwayoyi da tashe-tashen hankula a lokacin yaƙin neman zabe a jihar.
“Muna shirye-shiryen samar da yanayi na siyasa cikin lumana don aiwatar da duk harkokin zaɓe cikin lumana a jiharmu,” in ji shi.