
Wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya a Najeriya, Walter Mulombo ya bayyana cewa sama da Yan Najeriya 30,000 ne suke mutuwa a duk shekara sakamakon cututtukan da ke da alaƙa da shan taba sigari.
Ya bayyana haka ne a Abuja a yayin wani taro da aka shirya na yaƙi da shan taba, kamar yadda Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito.
Mista Mulombo ya ce mutanen da taba sigari ke kashewa ya zarta na waɗanda korona ta kashe a Najeriya inda ya ce taba na kashe mutum ne a hankali.