Home Siyasa Peter Obi ya gargaɗi magoya bayansa kan maja da Kwankwaso

Peter Obi ya gargaɗi magoya bayansa kan maja da Kwankwaso

0
Peter Obi ya gargaɗi magoya bayansa kan maja da Kwankwaso

 

Ɗan takarar shugaban Najeriya ƙarƙashin jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya gargaɗi magoya bayansa da su rinƙa haƙuri da ra’ayoyi mabambanta na ƴan Najeriya don kada hakan ya hana yin maja da wasu jam’iyyu a nan gaba.

Mista Obi ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda ya gode wa magoya bayan nasa dangane da irin haɗin kan da suke ba shi.

Jan kunnen nasa na zuwa ne yayin da rahotanni ke cewa yunurinsu na yin haɗaka da jam’iyyar NNPP da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, bai yi nasara ba saboda sun kasa daddalewa kan wanda za a mara wa baya a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

Ya bayyana cewa duk da an san halin da ake ciki a Najeriya na fushi da takaici, “ya zama wajibi a yi amfani da kuzarin da ake da shi wurin samun goyon bayan wasu da kuma haɗin kai”.

Obi ya yi kalaman ne bayan Rabiu Kwankwaso ya ce ba zai iya zama mataimakin wani ɗan takarar shugaban ƙasa ba a babban zaɓen 2023.

Waɗannan kalamai na Kwankwaso sun jawo ce-ce-ku-ce musamman a shafukan sada zumunta, inda magoyan Obi suka dinga sukarsa da kalamai marasa daɗin ji.