
Hukumar Jarrabawa ta Ƙasa, NECO ta ce ba za a yi jarrabawa a ranar 9 ga watan Yuli ba, sabanin raɗe-raɗin da wasu ke yi na cewa za a yi jarrabawa a ranar Eid-el-Kabir.
Majalisar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban jami’in yaɗa labarai da hulda da jama’a, Azeez Sani, ya rabawa manema labarai a Abuja a yau Litinin.
Ya ce hukumar tana sane da muhimmancin bukukuwan addini, don haka a ko da yaushe ta kan yi tsari da tanadin irin waɗannan ranekun wajen sanya ranar jarrabawa.
“hukumar ta aiyana mako guda ba jarrabawa, wanda ya fara daga ranar 8 ga watan Yuli zuwa 13 ga watan Yuli, a jarrabawar kammala makarantun sakandare (SSCE) da ke gudana ɗaliban da ke makarantu.
“An yi haka ne don baiwa Musulmai masu aminci damar samun isasshen lokaci yin bikin,” in ji shi.
Idan dai ba a manta ba a ranar 27 ga watan Yuni ne aka fara gudanar da jarabawar kammala makarantun sakandare ta shekarar 2022, SSCE, wadda za a kammala a ranar 12 ga watan Agusta.