
Ministan Tsaro, Bashir Magashi, ya bayyana cewa kimanin ƴan Boko Haram 64 ne da ake tsare da su a gidan gyaran hali na Kuje su ka tsere bayan harin da ƴan bindiga suka kai a daren jiya.
Magashi ya bayyana hakan ne a yau Laraba yayin da ya ke zantawa da manema labarai bayan ya kai ziyarar gani da ido a wajen.
Da yake bayar da alkaluman wadanda suka tsere, Magashi ya ce 600 daga cikinsu sun tsere yayin harin, inda ya ƙara da cewa am kamo 300 da ga cikin su, yayin da wasu kuma su ka samu nasarar tsere wa.
Ya ce: “An fara kai harin ne da misalin karfe 10:30 na dare. Da yawansu suka shigo gidan yarin kuma sun saki wasu daga cikin fursunonin da muke tsare kuma muna nan muna duba wa mu ga irin fursunonin da suka saka.
“Ba da jimawa ba, za mu ba ku ainihin adadin fursunonin da aka kama. Baya ga haka, muna ƙoƙarin ganin abin da za mu iya yi don ganin an dawo da duk wadanda suka tsere.
“ gidan yarin na daukar fursunoni kusan 994 sannan sama da 600 suka tsere. An sake kama mutane da dama kuma an mayar da su gidan yari. Wataƙila zuwa ƙarshen ranar, za a iya kama wasu kuma a dawo da su.
“Komai dai na daidaita. Mutanen da suka zo don yin wannan aika-aikin, daga bayanan, mun yi imanin cewa suna cikin wata ƙungiya ta musamman.
“Wataƙila ƴan Boko Haram ne saboda muna da adadin waɗanda ake zargi da Boko Haram sun tsare, kuma a halin yanzu ba za mu iya gano ko ɗaya daga cikinsu ba.
“Ina tsammanin su kusan 64 a gidan yarin kuma babu ɗaya daga cikinsu da yake samuwa duk sun tsere.”