
Rundunar Ƴan Sanda a jihar Nasarawa ta ce ta cafke wani fursuna guda ɗaya da ya tsere a harin da ƴan ta’adda su ka kai gidan yarin Kuje.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Ramhan Nansel, a madadin Adesina Soyemi, Kwamishinan Ƴan Sanda, CP, a jihar Nasarawa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ne ya samu labarin a yau Asabar a garin Lafiya na jihar Nasarawa.
Kakakin ya ce jami’an ƴan sandan reshen Keffi ne su ka kama wanda ya tsere ɗin bayan sun samu bayanan sirri.
“A ranar 9 ga Yuli, 2022 da misalin karfe 1:30 na safe, wani Hassan Hassan wanda sunansa da hotonsa na daya daga cikin wadanda suka tsere da zargin laifin ta’addancin Boko Haram, jami’an ‘yan sanda na rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa a Keffi sun sake kama shi.
“Hukumar CP ta bayar da umarnin mika wanda ake zargin zuwa wuri mafi aminci yayin da ake ci gaba da neman sauran wadanda suka tsere.
Sanarwar ta kara da cewa “Za a mika wanda ya gudu ga hukumar da ta dace domin daukar mataki.”
Ya ce CP din ya mika godiyarsa ga jami’an ‘yan sanda a jihar bisa kokarin da suke yi da kuma aikin da suke yi.
Sanarwar ta ce Soyime ya yi kira ga jama’a da su taimaka wa ƴan sanda da bayanai masu amfani idan har suka ga wasu suna gudu.