
Hukumar Kare Hakkin mai Sayen Kaya ta Jihar Kano, KSCPC ta ƙwace kimanin buhun fulawa 487, da ta lalace a wajen ajiyar kaya a kasuwar abinci ta duniya da ke Dawanau da ke birnin Kano.
Manajan-Darakta na riƙo a hukumar, Baffa Babba Dan’agundi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da kakakin hukumar, Musbahu Yakasai ya fitar a yau Talata a Kano.
Dan’agundi ya ce wasu mutanen kirki ne su ka bai wa hukumar bayanan sirri game da fulawar wacce aka kawo kasuwar da nufin sayar da ita.
Ya kara da cewa bayan an kai sumame wajen ajiyar fukawar a kasuwar Dawanau, gwajin da aka yi wa samfurin fulawar ya nuna cewa tuni ta daɗe da lalacewa.
Haka kuma ya ce hukumar ta su ta kama lemuka masu yawan gaske da suka lalace kuma ake sayar da su a kasuwar Sabon Gari da ke jihar.
Ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da bada bayanai a kan irin waɗannan lalatattun kayan, inda ya yi kira da a riƙa duba bayanin kayan masarufi kafin a yi amfani da shi.