
Kungiyar Marubuta Kare Hakkokin Dan Adam ta Najeriya, HURIWA, ta suffanta jam’iyya mai mulki ta APC a matsayin jam’iyyar siyasa ta ƴan ta’adda.
Jaridar Daily Post ta rawaito cewa HURIWA ta bayyana cewa yanzu lokaci ya yi da duk ƴan Nijeriya masu kishin ƙasa su ƙi amincewa da jam’iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Hakan ya biyo bayan fitowar Kashim Shettima a matsayin abokin shugaban kasa na jam’iyyar APC ga Bola Ahmed Tinubu.
A cewar HURIWA, Shettima ba komai bane illa mai ra’ayin riƙau na Islama da kuma kyamar kiristoci, inda ƙungiyar ta bayyana zaɓarasa a matsayin rashin adalci, rashin hankali, rashin kishin kasa da kuma saɓawa kundin tsarin mulki kuma ya nuna karara cewa masu kishin Islama da yan ta’adda na BOKO HARAM da ISWAP sun yi garkuwa da APC.
HURIWA ta kuma gargaɗi ƴan Nijeriya cewa duk kuri’ar da aka kaɗa wa jam’iyyar APC kuri’a ce ta raba kan ƙasar, ta na mai cewa a yanzu dole ne jama’a su zaɓi tsakanin jam’iyyun Labour Party, LP da kuma PDP.
HURIWA ta bayyana cewa gwamnatin musulmi da musulmi a halin yanzu da ake ciki a jihar Kaduna ta nuna karara cewa irin wannan tsarin baya goyon bayan kiristoci.
HURIWA ta ce irin wannan zaɓin da Tinubu ya yi ya zama nuna wariya ga waɗanda ba Musulmi ba kuma ya saɓa wa wasu sassan Kundin Tsarin Mulki na 1999 da aka gyara.