
Shahararren mawakin Nijeriya ɗin nan, Burna Boy ya baiyana nadamar dena kula takwaransa mawaki, Sound Sultan kafin ya rasu.
Burna Boy ya faɗi haka a wakar karshe ta sabon kundin waƙar da ya saki mai suna ‘Love, Damini’.
Mawakin ya yarda da cewa yana bukatar ya ƙara nuna ƙauna ga mutane yayin da suke raye.
Saƙon da ya faɗa a cikin wakar shine: “Da ma na yi magana da kaka na kafin lokaci ya ƙure.
“Da na sani na yi magana da Sound Sultan kafin ya mutu. Ya kamata in kara nuna wa mutane soyayya tun suna raye.
“Ya kamata in san yadda mutanena suke ji a ciki.
“Ina ƙoƙarin zama mutumin kirki, na yi ƙoƙari, na samu duka amma har yanzu ina takaici.”
A tuna cewa an tabbatar da mutuwar Sound Sultan a ranar 11 ga Yulin 2021 bayan ya yi fama da cutar daji a makogwaro.
Labarin mutuwarsa ya zo da kaɗuwa ga masoya da kuma ƴan ƙasa masu kishi.
Sound Sultan ya shahara tsakanin ƴan Nijeriya, inda ya fito da fitacciyar wakarsa mai suna ‘jagbajantis’ a shekarar 2000.