
‘
Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar AP a Jihar Delta, Sanata Ovie Omo-Agege, ya naɗa tsohon ministan harkokin Neja- Delta, Elder God’sday Orubebe, a matsayin Darakta-Janar na yakin neman zaɓensa.
Ima Niboro, Daraktan Sadarwa da Dabarun Yaɗa Labarai na ƙungiyar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja a yau Laraba.
Niboro ya ruwaito Mista Omo-Agege yana cewa an kawo Orubebe ne domin a kungiyar za ta amfana da ƙwarewarsa.
“Orubebe, tare da ni, zai jagoranci gudanar da ayyuka masu mahimmanci tare da tuntubar juna. Sannan jaruntakarsa, wanda zai kai ga jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).
“Tare da sauran tawagar, za mu nuna wa PDP hanyar fita daga gidan gwamnati a ranar 29 ga Mayu, 2023,” in ji shi.
Ya ce zaɓen ɗan siyasar, haifaffen kabilar Ijaw ya biyo bayan iliminsa da iyawarsa da kuma asalinsa.
“Kawo shi a tafiyar zai ƙarfafa yaƙin neman zaɓe kai tsaye kuma zai zaburar da masu ruwa da tsaki a fagen fafatawar da ke gaba,” in ji shi.