
Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gana da kwamitin sasanta wa da Farfesa Nimi Briggs ke jagoranta.
Shugaban ASUU na Ƙasa, Farfesa Emmanuel Osekede ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na ƙasa, NAN a jiya Talata a Abuja.
Gwamnatin Tarayya ta kafa Kwamitin Briggs a ranar 7 ga watan Yuni, domin ya sake tattaunawa da kungiyar ASUU a kan yarjejeniyar 2009 tare da mika rahotonsa ga ministan ilimi, Adamu Adamu cikin watanni uku.
Buhari , a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya fitar, ya ce “gaskiya ya ajiye dalibai a gida ya isa haka.”
Sai dai kuma Osedeke ya ce: “Ban fahimci dalilin da ya sa shugaban kasar ya ce “ya isa ba”, alhali ba mu ne mu ka janyo daliban ke ci gaba da zaman daɓaro a gida ba.
“Gwamnatin tarayya ta aiko da tawagarta domin tattaunawa da mu kuma mun gama. Maimakon ta dawo wurinmu ta faɗa mana sakamakon tattaunawar, sai kuma mu ke jin haka.
“Idan kun kafa kwamiti don tattaunawa a madadinku, kuma kwamitin ya gama kuma sun kawo muku bayanan ku sanya hannu sannan kuka ce yajin aikin ya isa haka, me wannan ke nufi,” inji shi.
Ya bukaci Buhari da ya gana da kwamitin tattaunawa da kuma sanya hannu kan rahoton.