
Mutum daya ya rasa ransa yayin da 84 suka samu raunuka a zanga-zangar bijire wa gwanati da ake yi a babban birnin Sri Lanka, Colombo, in ji jami’an asibiti.
Mutumin da ya mutu, mai shekara 26, ya rasu ne sakamakon matsalar numfashi, bayan da ‘yan-sanda suke ta harba wa masu tarzomar hayaki mai sa hawaye.
Wadanda suka ji raunin suna daga cikin wadanda suka yi cincirundo a kofar ofishin firaministan ne da kuma wadanda suke a kofar ginin majalisar dokokin kasar.
Bayan da Shugaba Gotabaya Rajapaksa ya tsere daga kasar, aka nada Ranil Wickremesinghea matsayin shugaban riko.
To amma kuma wannan mataki ya kara tunzara jama’a, inda suke neman shi ma sai ya sauka.
An sanya sabuwar dokar hana fita a yau Alhamis tun daga karfe 12 na rana har zuwa karfe biyar na Juma’a, kamar yadda wata sanarwa ta gwamnati ta bayyana.
Jama’a na zanga-zanga ne sakamakon matsin tattalin arziki mafi tsanani da kasar ta fada a tsawon gomman shekaru.
Al’ummar kasar da dama suna dora alhakin matsalar a kan gwamnatin Rajapaksa, kuma suna daukar Mista Wickremesinghe, wanda aka nada firaminista a watan Mayu a matsayin wani bangare na matsalar