Home Labarai Manomin da ya yi wa ‘yar shekara 8 fyade an yanke masa hukuncin daurin shekaru 3

Manomin da ya yi wa ‘yar shekara 8 fyade an yanke masa hukuncin daurin shekaru 3

0
Manomin da ya yi wa ‘yar shekara 8 fyade an yanke masa hukuncin daurin shekaru 3

Daga Hassan Y.A. Malik

A yau ne babbar kotun yanki da ke zamanta a Kasuwar Nama, Jos ta arewa ta yankewa wani manomi mai shekaru 25 mai suna Wundetenan Juna, da aka same shi da laifin yin fyade ga yarinya mai shekaru 8 zaman gidan kaso na shekaru 3.

Alkalin kotun, Yahaya Muhammad bai bawa wanda aka kama da laifin zabin biyan tara ba duk kuwa da kasancewar ya amince da ya aikata laifin da ake zarginsa da shi tare kuma da rokon kotu ta yi masa sassauci.

Mai shari’a Yahaya Muhammad a yayin yanke hukunci ya ce, wannan hukunci zai zama izina ga masu son aikata irin wannan laifi.

Tun da fari dai sai da mai shigar da kara, Mista O.S Ocho ya fadawa kotu cewa a ranar 2 ga watan Fabarairu ne dai aka shigar da kara ofishin ‘yan sanda ta Mangu kan faruwar lamarin inda daga baya kuma aka mika karar zuwa sashen binciken manyan laifuka ta jihar don ci gaba da bincike.

A waccan rana ta 2 ga watan Fabrairu ne dai Juna ya ja hankalin yarinyar mai shekaru 8 da haihuwa da N20, inda ya shigar da ita wani kango, inda a nan ne ya yi mata fyade.

Mai shigar da kara ya bayyana cewa, a yayin da a ke gudanar da binciken an samu raunika na kujewa a gaban yarinyar.

Mista Ocho ya bayyana kotu cewa laifin ya ci karo da sashen dokar Penal code na 285.