
Shahararriyar jarumar nan ta masana’antar Nollywood da ke kudancin Nijeriya, Ada Ameh ta rasu.
Jaridar The Nation ta jiyo cewa ta rasu ne a garin Warri da ke jihar Delta da misalin karfe 11 na daren jiya Lahadi, kamar yadda wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana a safiyar yau Litinin.
An ce Amah ta faɗi ne kwatsam lokacin da ta je wani kamfanin man fetur.
An tattaro cewa an garzaya da ita asibitin kamfanin man fetur na Najeriya amma ta rasu kafin a isa wurin.
Jaridar The Nation ta tattaro cewa jaruman kannywood da dama ne su ka riƙa tururuwa da safiyar yau Litinin don ganin gawar ta Ameh.
Ameh, wacce ta fito a matsayin Anita a cikin fim din ‘Domitilla’ a shekarar 1996, ta shahara da yin finafinan barkwanci, musamman a cikin shirin nan na barkwanci mai dogon zango, The Johnsons, inda ta ke fitowa da sunan Emuh.