Home Labarai Jirgin Dana ya yi saukar gaggawa a Abuja

Jirgin Dana ya yi saukar gaggawa a Abuja

0
Jirgin Dana ya yi saukar gaggawa a Abuja

 

 

 

An dakile wani babban ibtila’i a yau Talata bayan da jirgin Dana Air Boeing 737, mai lamba (5N DNA) ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe bayan da ya haifar da wata matsala a daya daga cikin injinansa.

Kamfanin jirgin ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau, inda ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:52 na rana kuma ba wanda ya samu wata matsala a cikin fasinjojin.

“Jirgin mu Boeing 737 da ke kan hanyar Abuja mai lamba (5N DNA) ya yi saukar gaggawa a yau, 19 ga watan Yuli, 2022, saboda wata matsala da ta afku a daya daga cikin injinansa,” in ji sanarwar.

“Matukin jirgin ya sanar da fasinjojin lamarin kuma ya saukar da jirgin lafiya a filin jirgin saman Abuja da misalin karfe 2:52 na rana.

“Dukkan fasinjoji 100 sun sauka lafiya kuma tawagar injiniyoyinmu sun dakatar da jirgin domin kulawa ta gaggawa.

“An kuma sanar da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) game da lamarin.”