
A yau Alhamis ne dai Majalisar Ƙoli ta Tsaro ta bayyana yiwuwar hana hawa babura da hakar ma’adinai a wani yunkuri na katse hanyoyin samar da kudade ga ƴan ta’adda a fadin ƙasar.
Taron, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta, ya samu halartar ministoci da wasu jami’an gwamnati, an yi shi ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Da ya ke zantawa da manema labarai a karshen taron, babban Lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, ya ce ‘yan ta’addan na fakewa ds hakar ma’adinai da hawa babura domin ta’addancin su.
A cewar Malami, ‘yan ta’addan na amfani da babura wajen tafiya su aikata ta’addanci tare da hako ma’adinai don samun kuɗaɗen sayen makamai.
Malami ya yi nuni da cewa, ƴan ta’adda sun tashi daga hanyoyin da suka saba amfani da su wajen samun kudaden gudanar da ayyukansu zuwa hakar ma’adinai da karbar kudin fansa, wanda hakan ya sa ya zama dole gwamnati ta dauki mataki.