Home Labarai Mata ta kashe mijinta da wuƙa a Adamawa

Mata ta kashe mijinta da wuƙa a Adamawa

0
Mata ta kashe mijinta da wuƙa a Adamawa

 

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wata matar aure mai suna Caroline Barka, ‘yar shekara 20, bisa laifin kashe mijinta, Barka Dauda, ​​da wuka har lahira.

Caroline Barka mazauniyar Angwan Tamiya ce a Ƙaramar Hukumar Madagali a jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Suleiman Nguroje, ya fitar a jiya Asabar a Yola.

Ya bayyana cewa ‘yan sanda sun kama wacce ake zargin ne a ranar Juma’a, biyo bayan rahoton da aka samu daga wani dan uwan ​​marigayin.

“fada ne ya ɓarke tsakanin wacce ake zargin, Caroline Barka, ‘yar unguwar Angwan Tamiya, a karamar hukumar Madagali, tda mijinta mai suna Barka Dauda, ​ bayan da mamacin ya dawo gida a bige, sai ya fada kan jaririnsu ɗan shekara guda yayin da aka kwantar da shi a kan gado.

“wannan shaye-shayen na sa, da yawan yin dare da kuma rashin sauke nauyinsa a matsayin miji,shine ya fusata wacce ake zargin ta kama marigayin da kokawa har ta kai ga ta daɓa wa mijin wuka.

“Sakamakon haka ya fadi a sume kuma daga baya aka garzaya da shi asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa,” in ji Mista Nguroje.