Home Labarai Buhari ya naɗa Nasiru Baballe-Ila a matsayin mataimaki kan al’amuran majalisar tarayya

Buhari ya naɗa Nasiru Baballe-Ila a matsayin mataimaki kan al’amuran majalisar tarayya

0
Buhari ya naɗa Nasiru Baballe-Ila a matsayin mataimaki kan al’amuran majalisar tarayya

 

 

 

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da naɗin Nasiru Baballe-Ila a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin majalisar wakilai ta kasa.

Garba Shehu, mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai ne ya tabbatar da nadin a cikin wata sanarwa a jiya Lahadi a Abuja.

Baballe-Ila, wanda ya yi karatu a Victory College, Alexandria da kuma West London College da ke tarayyar Birtaniya, ya kasance hamshakin dan kasuwa mai sha’awar harkar hada-hadar fataucin fata kafin ya shiga harkokin siyasa.

A shekarar 2011 da 2015, an zabe shi a matsayin dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Tarauni a Kano.

A cewar mai Garba Shehu, Nasiru Baballe Ila ya maye gurbin Umar El-Yakub wanda shugaban kasa ya naɗa a matsayin minista.