
Shelkwatar Tsaro ta Ƙasa ta bayyana cewa Dakarun ‘Operation Safe Haven’ sun kama wasu da ake zargin dillalan bindiga ne guda 3 da kuma masu garkuwa da mutane biyu a sassa daban-daban na jihar Plateau,
Darakta mai kula da ayyukan yaɗa labarai na tsaro, Maj.-Gen. Bernard Onyeuko ne ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin a Abuja.
Onyeuko ya ce a ranar 24 ga watan Yuli ne sojojin suka kama dillalan bindiga uku a wani samame da suka kai kauyen Shimakar da ke Ƙaramar Hukumar Shendam a jihar.
Ya bayyana sunayen wadanda ake zargin da Julius Simon (wanda aka fi sani da Bagga) ɗan shekara 37; Wolta Zambai mai shekaru 45 da Iliya Peter (wanda ake kira Doubok) ɗan shekara 27.
A cewarsa, a halin yanzu ana ci gaba da binciken wadanda ake zargin.
Onyeuko ya ce a ranar ne sojojin suka kuma kama masu garkuwa da mutane biyu masu suna Musa Usman, ɗan shekara 27 da Adam Mohammed mai shekara 25 a Barkin Ladi.
Ya ce wadanda ake zargin sun amsa laifin yin garkuwa da mutane da dama a yankin, ciki har da yin garkuwa da wani Jeremiah Iliya mai shekara 6 a ranar 21 ga watan Yuli, inda ya kara da cewa wadanda ake zargin suna hannun sojoji ana ci gaba da yi musu tambayoyi.