
An sallami Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo daga asibiti bayan an yi masa aiki a ƙafarsa.
Babban liktia na musamman na mataimakin shugaban kasar, Nicholas Audifferen ne ya shaida haka.
Kakakin Osonbajo ɗin, Laolu Akande ne ya fadi ta bakin Audifferen a wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin a Abuja.
Ya ce an sallami Osinbajo ɗin ne bayan an yi masa aiki lafiya lau a asibitin Duchess International Hospital da ke Legas.
Ya ƙara da cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa ɗin ya shafe mako daya. Asibitin kafin a sallame shi, inda ya ce yana samun sauki sosai.