
Kungiyar Dillalan Jakuna, DDA, ta ce shirin haramta yanka jakuna a kasar nan zai haifar da rasa ayyukan yi ga ‘yan Najeriya sama da miliyan uku.
Shugaban kungiyar na kasa, Ifeanyi Dike ne ya bayyana hakan a wajen wani taron kwana ɗaya da aka gudanar kan wasu kudirori takwas na ɓangaren noma.
Taron jin ra’ayoyin jama’a, wanda ya gudana a yau Litinin, kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin noma da raya karkara a karkashin Sanata Bima Enagi ne ya jagoranta.
Kudirin mai suna: “Kudirin Dokar Kula da yankan Jaki da yin lasisin fitar da shi ƙasashen ƙetare ta 2020” wanda kuma Sen. Yahaya Abdullahi ya gabatar da shi.
Kudirin doka wanda ya tsallake karatu na biyu a ranar 6 ga Yuli, 2021 yana da nufin rage ƙarewar jinsin jakuna, duba da gudunmawarsa ga muhalli, ilimi, tarihi, nishaɗi da kimarsu ga al’umma.
Haka kuma ƙudirin na neman ayyana jakuna a matsayin wani nau’in dabbobi masu haɗari saboda yanka su da a ke yi ba bisa ka’ida ba da nufin safarar fatun r jikinsu, ya janyo wa garken dabbobin kasa cikas matuka.
A nasa jawabin, Dike ya ce dokar hana yankan jaki kai tsaye ba ita ce mafita ba wajen kawar da jakunan da ake tunanin kashewa a kasar.
“Ya kamata mu sani cewa ganawar kai tsaye kamar yadda wannan kudiri ya gabatar zai haifar da wasu kungiyoyin fasakwauri masu karfi wadanda suka dukufa wajen samun kayayyakin jakin da ake fitarwa zuwa kasar Sin ta yadda za su yi zagon kasa ga tattalin arzikin kasar.