
Kotu ta bayar da belin Beatrice Ekweremadu, matar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya Ike Ekweremadu a shari’ar da ake yi musu a birnin London
Ana yi wa Mista Ekweremadu, dan majalisar dattawan Najeriya da ka wakiltar Enugu ta yamma, tare da matarsa shari’a ne bisa zargin cire sassan jikin dan Adam a wata kotu da ke Burtaniya.
Jaridar The Cable, ta ruwaito cewa kotun ta bayar da belin Beatrice Ekweremadu ne bayan da ta bayyana a gaban kotun da ke birnin London.
To sai dai kotun ta hana belin mijin nata Mista Ekweremadu.
Ike Ekweremadu, mai shekara 60, da matarsa Beatrice Nwanneka Ekweremadu, mai shekara 55, sun gurfana a gaban kotun Majistiret ta yankin Uxbridge a Yammacin London.