
Muhammad Abacha, ɗan takarar gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar PDP, tsagin Shehu Wada Sagagi, ya maka Sadeeq Wali, Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC da kuma Jam’iyyar PDP a gaban kotun tarayya da ke zamanta a Kano.
Abacha, wanda ɗan tsohon shugaban ƙasa na soji, Janar Sani Abacha (mai ritaya) ne, bisa zargin hana shi yiwa jam’iyyar takara bayan ya lashe zaɓen fidda-gwani na ɓangaren Sagagi, wanda shine kotu ta amince da ya ci gaba da shugabancin jam’iyar har zuwa Disambar 2024.
Sai dai kuma da INEC ta fitar da sunayen ƴan takarar gwamna a jihar Kano a makonni biyu da suka gabata, sai ta fitar da sunan Sadiq Wali, ba na Abacha ba, lamarin da ya sanya ya garzaya kotu.
A cikin ƙunshin ƙarar, Abacha ya roƙi kotun ta haramtawa Wali kiran kansa a matsayin ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP.
Ya kuma roki kotun da ta tilasta wa INEC da ta ayyana sunan Muhammad Abacha a matsayin ɗan takarar jam’iyyar, inda ya kuma buƙaci kotun da ta umarci PDP ta warware naɗin da ta yiwa Wali a matsayin ɗan takarar gwamna a jam’iyyar.