Home Labarai Ƴan majalisar wakilai sun bi sahun sanatoci kan barazanar tsige Buhari

Ƴan majalisar wakilai sun bi sahun sanatoci kan barazanar tsige Buhari

0
Ƴan majalisar wakilai sun bi sahun sanatoci kan barazanar tsige Buhari

 

 

Shugabannin bagaren marassa rinjaye a Majalisar Wakilai ta Najeriya sun bi sahun takwarorinsu na Majalisar Dattawa, wajen bai wa Shugaba Muhammadu Buhari wa’adin mako shida na ya magance matsalar tsaro ko kuma su tsige shi.

Shugaban marassa rinjaye a majalisar Ndudi Elumelu, shi ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa ta sirri da takwarorinsu sanatoci a jiya Alhamis.

Honorabul Elumelu ya ce muddin shugaban ya kasa daukar kwakkwaran mataki da za a ga sauyi a halin tsaron da ake ciki a kasar, za su fara daukar matakin tsigewar.

Bayan matsalar ta tsaro, shugaban marassa rinjayen ya kuma ja hankalin gwamnatin kan yanayin da kasar gaba daya take ciki, abin da ya hada da batun faduwar darajar Naira a kan kudaden waje da kuma matsalolin bangaren sufurin jirgin sama.

A ranar Laraba ‘yan Majalisar Dattawa yawanci daga bangaren marassa rinjaye suka fice daga zauren majalisar, bayan da shugaban marassa rinjayen Philip Aduda ya nemi shugaban majalisar Ahmed Lawan ya ba shi damar gabatar da bukatar tattauna batun tsaron da kuma neman tsige Shugaba Buhari.

A lokacin shugaban majalisar ya ki ba shi damar tare da cewa bukatar ba ta dace ba sam-sam, lamarin da ya harzuka marassa rnjayen suka fice daga zauren.

Bayan nan ne suka bayyana cewa sun ba shugaban kasar wa’adin mako shida ya shawo kan matsalar tsaron ko kuma ya fuskanci tsigewa.