
Hukumar gudanarwar kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ta shawarci dukkanin jami’ai da ma’aikatanta da su yi taka-tsan-tsan tare da kiyayewa kan duk wasu wurare da hanyoyi da suke bi saboda halin tsaron da ake fama da shi a fadin Najeriya a yanzu.
BBC Hausa ta rawaito cewa a wata sanarwa hukumar ta bayyana cewa bayanan sirri sun yi gargadin cewa akwai shirin da bata-gari ke yi na shiga sassan kasar musamman manyan biranen jihohi, da suka hada da babban birnin tarayya Abuja domin aikata miyagun ayyuka.
Ayyukan da suka hada da satar mutane domin karbar kudin fansa da kuma daukar sabbin mabiya domin gudanar da ayyukan ta’addanci.
Hukumar ta bayar da wasu shawarwari na tsaro ga jami’an nata kan yadda za su gudanar da harkokinsu a duk inda suke domin kauce wa fadawa cikin matsalar tsaron.
Sai dai ta bukaci da kada su tayar da hankali tana mai ba su tabbacin cewa hukumomin tsaron Najeriyar na yin duk abin da ya kamata kan kalubalen.