
Wata kotun majistare da ke Kano a jiya Juma’a, ta bayar da umarnin a tsalala wa wani tela mai shekaru 20, Abubakar Sani bulala 12 bisa samun sa da kwalbar maganin tari mai ɗauke da sinadarin ‘codeine’ guda daya.
Sani, wanda ke zaune a unguwar Fagge a jihar Kano, an yanke masa hukuncin ne bisa laifin takur wa al’umma da kuma mallakar maganin codeine.
Alkalin kotun, Farouk Ibrahim Umar ya kuma yanke wa Sani hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni biyu ba tare da zaɓin tara ba.
Tun da fari, lauyan masu shigar da kara, Aminu Dandago, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Yuni a unguwar Fagge.
Ya ce a wannan ranar, da misalin karfe 9 na dare, tawagar ƴan sandan da ke aiki a Caji-ofis na Fagge, Kano, ta kama Sani a lokacin da yake sintiri a cikin unguwa.
Rundunar ‘yan sandan ta ce an kama Sani ne da kwalba ɗaya na maganin codeine da ake zargin yana cikin maye.