Home Labarai Ƴan bindiga sun ɗauke jaruman Nollywood 2 a Enugu

Ƴan bindiga sun ɗauke jaruman Nollywood 2 a Enugu

0
Ƴan bindiga sun ɗauke jaruman Nollywood 2 a Enugu

 

 

Rahotanni na nuni da cewa wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da jaruman masana’antar finafinai ta Nollywood, kuma mambobi a Ƙungiyar Jaruman Fim ta Ƙasa, AGN, Cynthia Okereke da Clemson Cornel, wanda a ka fi sani da Agbogidi a Jihar Enugu.

Daraktar yaɗa labaran ƙungiyar, Monalisa Chinda ce ta bayyana hakan a wata sanarwar da ta fitar a jiya Juma’a.

Bayan da ta yi kira ga jami’an tsaro da su gaggauta kuɓutar da jaruman, Chinda ta kuma ce Shugaban AGN, Ejezie Emeka Rollas ya umarci jaruman masana’antar da su dena zuwa wajen jihar ɗaukar fim har sai sun samu tsakiyar jami’an tsaro.