Home Siyasa INEC ta rufe yi wa ƴan Najeriya rijistar zaɓe a jiya Lahadi

INEC ta rufe yi wa ƴan Najeriya rijistar zaɓe a jiya Lahadi

0
INEC ta rufe yi wa ƴan Najeriya rijistar zaɓe a jiya Lahadi

 

 

Ƴan Najeriya da dama suna ƙorafi kan rashin samun damar yin rijistar zaɓe, bayan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta rufe yin rijistar a jiya Lahadi.

INEC ta ce ba za ta sake buɗe ci gaba da yin rijistar ba, bayan da ta tsawaita hakan a baya.

Sai dai rahotanni sun ce ko a jiya Lahadin wuraren da ake yin rijistar sun yi cikar kwari, amma har ma’aikatan INEC suka tashi mutane da dama ba su samu yi ba.

Tun a watan Yunin shekarar 2021 ne INEC ta fara yi wa ƴan Najeriya rijistar, sai dai duk da hakan ba a kai ga kammalawa ba.