
Ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyar PDP, Atiku Abubakar ya naɗa Lynne Bassey a matsayin mataimakiya ta musamman kan harkokin da ci gaban mata da matasa.
A wata sanarwa da mai baiwa Atiku shawara kan yaɗa labarai, Paul Ibe ya fitar, ya ce naɗin na Bassey zai fara aiki ne a yau 1 ga watan Agusta.
Ibe ya ƙara da cewa naɗin na Bassey shine na biyar da Atiku ya sanar a yan makonnin da suka gabata.
Ya ce naɗin na Bassey ya yi nuni da cika alƙawarin da Atiku ya yi na sanya mata da matasa a gwamnatin sa idan ya ci zaɓe.
Bassey ta kammala karatunta a Jami’ar Calabar, inda a yanzu haka table yin karatun digirin digirgir a Jami’ar Pan Atlantic, Makarantar Koyon Kasuwanci ta Legas.