
Bayan rantsuwa da gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai yayi cewa sai ya fatattaki duk wani malamin Jami’ar Jihar Kaduna, KASU, da ya cigaba da yajin aiki, Malamai sun dawo aiki gadangadan a jiya Litinin.
Rahotanni da suka iske PREMIUM TIMES Hausa sun nuna yadda ɗalibai suka yi tururuwa zuwa jami’ar domin cigaba da karatu.
Sai dai kuma ba karatu a ka yi ba a wannan rana, inda ɗaliban sun ci gaba da jarabawa ce wacce suna tsaka da zana wa a ka tafi yajin aikin.
Dalibai sun garzaya dakunan karatu duk sun zauna domin fara rubuta jarabawa.
Idan ba a manta ba a cikin makon jiya gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya yi rantsuwar cewa duk malamin da ya shiga yajin aikin malaman jami’o’i zai fuskanci hukuncin gwamnati.
” Na rantse duk malamin da ya shiga yajin aiki zan kore shi aiki. Domin jami’ar gwamnatin jiha ce KASU ba ta gwamnatin Tarayya ba. Mune muke biyan su albashi saboda haka dole su koma aiki. Wanda kuma yaki zai gani a akwanan sa.
” Sannan kuma za mu duba duk wanda ya karbi albashin mu kuma ya yi yajin aiki a baya zai biya mu idan muka gano haka.
Har yanzu malaman Jami’o’i na cigaba da yajin aikin a fadin kasar nan. Sun fara yajin aiki tun daga watan Faburairu har yanzu.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci ministan Ilimi da ya saka baki sannan ya gaggauta ganin an samu maslaha tsakanin malaman da gwamnatin cikin gaggawa domin dalibai su koma karatu.
Da yawa daga cikin iyaye sun fara cire ya’ayn su daga jami’o’in gwamnati suna maida su jami’oi masu zaman kansu.